21 Oktoba 2021 - 16:03
​Najeriya: Turkiya Da Najeriya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyi Har Guda 8 A Ziyarar Erdogan Zuwa Abuja

Shugaban tarayyar Najeriya Mohammadu Buhari ya yabawa shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan tare da matarsa wadanda suka kai ziyarar aiki na kwanaki biyu a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa a cikin kwanaki biyu da ya yi a tarayyar Nageriya shugaban kasar Turkiyya ya bude cibiyar raya al’adu ta kasar Turkiyya a birnin Abuja, sannan an sanya hannu a kan yarjeniyoyi daban-daban har guda 8 tsakanin kasashen biyu.

Banda haka shugaba Erdogan ya gana da yan kasuwan Najeriya karkashin kwamitin kasuwancin tsakanin kasashen biyu. A na shi bangaren shugaba Buhari ya yabawa shugaba Erdogan da shirinsa na daukar nauyin yan gudun hijira miliyon 4 daga kasashen Siriya, Afganistan da Iraki.

342/